Cp Muhammad Wakili "Singham" Ya Karyata Wasu Rahotanni Akan Cewa Ya Rasu

 Tsohon kwamishinan ƴan sandan jihar Kano da ke Najeriya CP Muhammad Wakili, ya ƙaryata wasu rahotanni da ke cewa Allah ya yi masa rasuwa yayin wani hatsarin mota.Da daren ranar Talata ne wasu labarai da ke bayyana rasuwarsa sakamakon hatsarin mota suka bazu a shafukan sada zumunta, inda mutane suka riƙa sanya hotunansa, suna fatan Allah ya ji ƙansa.


Sai dai yayin zantawa da BBC, CP Muhammad Wakili mai ritaya, ya ce yana nan da ransa, cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali.


"Ban san ta ina wannan labari ya fito ba, ban san mene ne dalilinsu ba, ban san me suke son su cimma da wannan abu ba, wannan al'amari ya sa mutane damuwa, tun 11 na dare ake ta kira na domin a tabbatar da gaskiyar wannan labari," in ji tsohon kwamishinan 'yan sandan wanda aka fi sani da Singham.


Cp Muhammad Wakili "Singham" Ya Karyata Wasu Rahotanni Akan Cewa Ya Rasu Cp Muhammad Wakili "Singham" Ya Karyata Wasu Rahotanni Akan Cewa Ya Rasu Reviewed by MR MB on 1:13 AM Rating: 5

No comments:

ismaeeelkwr. Theme images by Sookhee Lee. Powered by Blogger.