Zaa Cigaba Da Sulhu Tsakanin Taliban.

 Tawagar wakilan gwamnatin Afghanistan ta shirya barin Kabul zuwa Qatar domin fara zagaye na biyu na tattaunawa da 'yan Taliban da nufin kawo ƙarshen yaƙin da ake yi na shekara da shekaru.


An soma tattaunawar cikin watan Satumba a birnin Doha amma kuma yaƙi ya ci gaba da ƙazanta.


Gwamnatin Afghanistan na neman a tsagaita wuta amma kungiyar Taliban ta ce za a yi sulhu ne kaɗai idan aka samu ci gaba a tattaunawar.


Masu taimaka wa zaɓaɓɓen shugaban Amurka Joe Biden sun bayyana ƙarara cewa suna son ganin muhimmin ci gaba idan Amurkar za ta janye ragowar dakarunta nan da watan Mayu


Source:Bbc Hausa.

Zaa Cigaba Da Sulhu Tsakanin Taliban. Zaa Cigaba Da Sulhu Tsakanin Taliban. Reviewed by MR MB on 12:33 AM Rating: 5

No comments:

ismaeeelkwr. Theme images by Sookhee Lee. Powered by Blogger.