Wasu mawaƙan Najeriya sun shiga ƙungiyar maza marowataWasu daga cikin manyan mawaƙan Najeriya sun shiga kungiyar maza marowata da ake yi wa laƙabi da Stingy Men Association of Nigeria.

Wannan ƙungiya dai na ta samun karɓuwa musamman a shafukan Facebook da Twitter.

A wani saƙo da mawaƙi Don Jazzy ya wallafa, an ga hoton katinsa na ƙungiyar wanda mutane da dama suka yaɗa a Twitter.Shi ma mawaƙin Najeriya da ke zaune a Landan, Mr Eazi ya wallafa katinsa na zama ɗan ƙungiyar a shafin Twitter.


A ranar Litinin ne aka fitar da shafin ƙungiyar a Twitter:


Mutane da dama a shafin Twitter na ta wasa da raha kan lamarin, inda suka ce za su ƙirƙiri taken ƙungiyar da kuma inda hedikwatarta za ta kasance.

Babu wani tabbaci kan yadda aka fara tattauna wannan batu a Najeriya, sai dai a halin yanzu ana ta tattauna shi a Afrika.


Source: BBC hausa

Wasu mawaƙan Najeriya sun shiga ƙungiyar maza marowata Wasu mawaƙan Najeriya sun shiga ƙungiyar maza marowata Reviewed by Extraordinary on 10:12 PM Rating: 5

No comments:

ismaeeelkwr. Theme images by Sookhee Lee. Powered by Blogger.