Gwamnatin Najeriya Tabada Daman Rage Kudin Wutan Lantarki.

 Ma'aikatar da ke kula da harkokin wutar lantarki ta Najeriya ta dakatar da wani ƙarin kuɗin wuta da aka yi, bayan barazarar da kungiyoyin ƙwadago suka yi na sa-kafar-wando-guda da gwamnati.

A wannan makon ne aka sanar da ƙarin farashin, wanda mahukunta suka danganta da hauhawar farashi, inda kilowatt ɗaya ya tashi daga naira biyu ya koma naira huɗu.


Ma'aikatar wutar ta hanzarta sanar da janye karin kuɗin wutar da aka yi ne, kamar yadda ta ce domin ta fahinci cewa an jahilci ƙarin, saboda wasu na cewa ya kai kashi hamsin cikin ɗari, alhali, ƙarin yana da nasaba ne da hauhawar farashi, kuma doka ce duk bayan wata shida, hukumar da ke kula da harkokin wutar lantarki da sauran ɓangarorin da abin ya shafa, kan yi nazarin halin da ake ciki domin daidaita ƙarin da ya dace.


Mai taimaka wa ministan wutar lantarki Injiniya Sale Mamman kan hulda da jama'a Ado Adamu Also ya ce gwamnati ta dakatar da ƙarin ne ganin cewa akwai tsohuwar jayayyar da ƙungiyar ƙwadago ke yi da gwamnati dangane da wani tsohon ƙarin farashi da ba a cim ma maslaha ba tun watan Satumban bara.


Tun lokacin da maganar karin kudin wutar ta fito, ƙungiyar ƙwadagon Najeriya da wasu dangoginta da ke fafutukar kare haƙƙin masu amfani da wutar lantarkin suka yi ta kumfar-baki, suka fara ta da ƙura.


Source:BBC HAUSA.

Gwamnatin Najeriya Tabada Daman Rage Kudin Wutan Lantarki. Gwamnatin Najeriya Tabada Daman Rage Kudin Wutan Lantarki. Reviewed by MR MB on 4:26 PM Rating: 5

No comments:

ismaeeelkwr. Theme images by Sookhee Lee. Powered by Blogger.